An nada tsohon dan wasan Najeriya, Micheal Nsien, a matsayin sabon kocin kungiyar maza ta ‘yan kasa da shekaru 16 ta Amurka.
Nsien shi ne ya jagoranci kungiyar ta USL Championship, FC Tulsa.
Dan wasan mai shekaru 41 ya wakilci Najeriya a matakin U-23.
Tsohon mai tsaron baya kuma ya taba horar da Tulsa Roughnecks.
Nsien ya buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Major League Soccer, LA Galaxy da Portland Timbers a lokacin aikinsa
“Yana da gata shiga US Soccer a matsayin kocin na U-16 Men’s Youth Team na kasa,” ya gaya wa shafin yanar gizon USSF.
“Damar yin aiki tare da shugabannin wasanni a kasarmu dama ce mai ban mamaki. Ina matukar farin cikin samun damar taimakawa wajen jagorantar mafi kyawun ’yan wasan kasarmu masu tasowa yayin da suke kaddamar da ayyukansu. ”
Usien ne zai jagoranci kungiyar a karon farko a gasar cin kofin kwallon kafa da Spain za ta karbi bakunci daga ranar 16-28 ga watan Nuwamba.