Kamar yadda muka bayyana muku tun farko cewa Mohammad Mokhber ne zai zama shugaban riƙon ƙwarya na gwamnatin Iran, to a yanzu jagoran addinin ƙasar Ayatollah Khamenei ya sanar da hakan a shafinsa na X.
Ya ce Mokhber zai hada kai da sauran bangarorin gwamnati – ‘yan majalisa da kuma masu shari’a domin tabbatar da an gudanar da zaben sabon shugaban ƙasa a cikin kwanaki 50 masu zuwa.