Hajiya Hauwa Kulu Kyari, matar marigayi shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, ta zama “Gimbiya” ta Farko a Jama’are.
Alhaji Nuhu Wabi III, Sarkin Jama’are ne ya yi bikin nada ta ranar Lahadi a fadarsa.
Da yake jawabi a wajen bikin, Sarkin ya bayyana ta a matsayin “Yar Jama’are ta gaskiya wadda ta yi kokari wajen ci gaban masarautar baki daya”.
“Al’adar Gimbiya ‘yar Sarki ce kuma mai alaka tsakanin sarki da mata, wadanda ba su da damar shiga harkokin hukumomin gargajiya kai tsaye.
“Da wannan nadin, matan Jama’ar yanzu suna da wakili a Majalisar Masarautar, yanzu ana iya jin muryoyinsu karara.
“Na cika cewa yanzu ina da ‘yar Masarautar ta gaske a Majalisar.
“Ta cancanci a san ta saboda ta mallaki dukkan dalilai guda uku da aka san mutane da rawani a masarautar.
“Wannan ya hada da kwazo a wani fanni na musamman, bayar da gudunmawa mai ma’ana ga ci gaban Masarautar da zama na gidan sarauta.