Hukumomi a Koriya ta Kudu sun tabbatar da naɗin firaministan Koriya ta Kudu a matsayin shugaban ƙasar na riƙo.
A jawabina na farko bayan naɗinsa, Han Duck-soo ya ce abin da zai mayar da hankali a kai shi ne ”daidaita al’amura a ƙasar tare da kwantar wa jama’a hankali”.
“A matsayina na ɗan’adam da ya damu da al’amuran ƙasarmu, ina amfani da wannan dama wajen bai wa mutanen Koriya haƙuri,” in ji Han.
Shugaban riƙon ya ce zai yi duk mai yiwuwa don ganin ƙasar ta inganta al’amuran ƙasar. In ji BBC.