Jami’an tsaron sintiri na Amotekun jihar Oyo, ta ce, ta miƙa fasinjoji 147 ƴan Arewa da ta kama ga jami’an ƴan sanda a Ibadan ranar Talata, ga jami’an tsaro a jihar Ogun.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ya fitar.
Sai dai binciken farko ya gano cewa, ba a same su da wasu kayayyaki da suka zama barazana ga zaman lafiya ba.


