Wata kungiyar likitoci a Sudan ta ce asibitoci 39 cikin 59 ne aka lalata a Khartoum, babban birnin ƙasar yayin da faɗa da ya ɓarke a ƙasar ke shiga kwana ta biyar.
Cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar yau Laraba, ta ce asibitoci 20 kaɗai ne gudanar da aiki.
“Cikin asibitoci da suka daina aiki, akwia tara waɗanda bam ya lalata da kuma wasu 16 da aka tilasta wa tashi daga wajen da suke,” in ji kungiyar.
Ana ci gaba da gwabza faɗa a birnin Khartoum da wasu sassan Sudan, yayin da sojojin gwamnati da dakarun RSF ke ci gaba da zargin juna da saɓa wa yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta ta sa’a 24 da ya kamata ta fara aiki da yammacin jiya Talata.