Gwamnati ta kwashe ‘yan Najeriya kimanin 542 da suka makale a kasar hadaddiyar Daular Larabawa.
A wani sako ta Hukumar da ke kula da lamurran ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje ta wallafa a shafinta na Tuwita, ta ce da misalin karfe 4:29 na asubahin yau ne jirgin da ya kwaso mutanen ya sauka a filin jirgin saman Abuja babban birnin kasar.
Wannan na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da hukumar shige da fice ta kasar Hadaɗɗiyar Daular Larabawa ta bayyana dakatar da bai wa ‘yan Najeriya biza, saboda wasu matsaloli da suka shafi diplomasiyya tsakanin kasashen biyu.
Rahotonni sun ambato gwamnatin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa na cewa duka wadanda suka cika takardun neman biza za a mayar musu da takardunsu ba tare da samun amincewa ba.
Ta kuma ce ”kin amincewar ya shafi kowanne dan Najeriya, dan haka babu wanda za a ba shi biza a halin yanzu”.
A baya-bayan nan dai dangantaka na kara yin tsami tsakanin kasashen biyu, inda a watan da ya gabata kasar ta UAE ta daina bayar da bizar yawon bude ido ga ‘yan kasa da shekara 40, lamarin da ya shafi ‘yan Najeriya da na wasu kasashen.
Haka kuma a shekarar 2021 ma ƙasashen biyu sun shafe watanni masu yawa suna ce-ce-ku-ce game da harkar sufurin jiragen sama