Ƙungiyar likitoci ta ƙasar Indiya (FAIMA), ta ce an garzaya da ɗalibai masu karatun likitanci 50-60 zuwa asibiti bayan da jirgin Air India da ya yi hatsari ya faɗa kan gidan kwanan ɗaliban.
Ƙungiyar ta kuma ce a yanzu akwai ɗalibai guda biyar da ba a san inda suke ba, yayin da guda biyu kuma an shiga da su ɗakin kula da waɗanda ke cikin matsanancin hali.
Haka nan akwai ƴan’uwan wasu likitocin da su ma ba a san inda suke ba bayan hatsarin.
Ƙungiyar likitocin ta Indiya ta ce yawancin fasinjojin jirgin da aka garzaya da su asibiti an kai su ne a mace.