An fitar da firaministan Japan, Fumio Kishida bayan an ji ƙarar fashewar wani abu lokacin da yake gab da fara jawabi .
Mista Kishida dai bai ji wani rauni ba.
‘Yan sanda a birnin Wakayama sun cafke wani mutum da ake zargin shi ne ya jefa wani abin fashewa mai hayaƙi.
Rahotanni sun ce an ji wata ƙara kuma an ga hayaƙi yana tashi a wurin da aka tsara firaministan zai yi jawabi, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta Japan NHK ta bayyana.
Yanzu ne dai bayanai ke ci gaba da fitowa kan lamarin da ya faru a birnin na Wakayama.
Hotunan bidiyo sun nuna wasu jami’ai na kawar da komai sannan suna fitar da wani mutum daga wurin da aka ji fashewar, sannan an ga mutane a tsorace.


