A ranar Asabar din da ta gabata ne wasu ‘yan ta’adda suka kai hari kan al’ummar Dogon-noma da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna, inda suka yi garkuwa da mata 15 da namiji guda.
Wani mazaunin kauyen mai suna Istifanus, ya shaidawa manema labarai cewa da yawa daga cikin mazauna kauyen sun gudu zuwa yankunan da ke makwabtaka da su domin tsira da rayukansu a lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari tare da harbe-harbe.
“Za mu iya tabbatar da adadi da yamma lokacin da za mu iya shiga ƙauyen. Maharan sun mamaye kauyen ne da misalin karfe 5:30 na safiyar ranar Asabar din nan da yawan gaske, inda suka rika harbi ba kakkautawa.
Wani tsohon shugaban karamar hukumar, Cafra Caino ya ce ba za a iya tantance adadin wadanda suka mutu ba.
“Har yanzu ba mu sami adadin wadanda suka mutu ba saboda mutanen yankin sun yi gudun hijira a lokacin da maharan suka mamaye al’umma. Al’ummar, wani lokaci a shekarar 2019, sun fuskanci mummunan hari inda aka kashe mutane 74 kuma a baya-bayan nan al’umma na fuskantar hare-hare,” inji shi.
A halin da ake ciki, rundunar ‘yan sandan ta kasa samun martani kan lamarin.