An yanke wa tsohon firaministan Pakistan, Imran Khan da matarsa Bushra Bibi hukuncin ɗauri na shekara 14, hukunci na biyu da aka yanke wa tsohon Firaministan cikin kwana biyu.
An samu ma’auratan da laifin cin gajiyar kyautukan gwamnati ba bisa ka’ida ba – mako guda kafin babban zaben da aka hana shi tsayawa takara.
Khan, wanda abokan hamayyarsa suka hamɓarar da shi a matsayin firaminista a shekarar 2022, ya riga ya yi zaman gidan yari na shekaru uku bayan samun shi da laifin cin hanci da rashawa.
Ya ce yawancin ƙararrakin da ake yi masa bita da kullin siyasa ne.
Shari’ar ta ranar Laraba ta shafi tuhume-tuhumen da ake yi masa ne a kan wasu kyaututtukan gwamnati da aka yi masa da matarsa a lokacin da suke kan karagar mulki, yayin da kuma shari’ar ta ranar Talata – wadda aka yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 10 a kan zargin fallasa wasu bayanan sirri na ƙasar.
Ana tunanin hukunce-hukuncen biyu za su gudana a lokaci guda, kodayake ba a tabbatar da hakan ba.
Kotun ta kuma umarci ma’auratan da su biya tarar kuɗi rupe biliyan 1.5, dalar Amurka 5.3m ke nan.
Lauyoyin Khan sun ce za su daukaka kara zuwa babbar kotun Pakistan kan shari’o’in biyu.