fidelitybank

An kuma cafke Dan Bindiga yayin tafiya aikin Hajji

Date:

Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, sun bayyana cewa sun kama wani dan fashi da makami mai garkuwa da mutane a Sokoto yayin da ake tantance maniyyata mahajjata.

Wanda ake zargin, kamar yadda Aminiya ta ruwaito, mai suna Sani Galadi, an kama shi ne a ranar Litinin a filin jirgin saman Sultan Abubakar da ke Sakkwato, bayan da jami’an ā€˜yan sanda suka bi shi.

Kamen na zuwa ne kimanin sa’o’i 24 bayan da jami’an tsaro suka kama wani da ake zargin dan fashi da garkuwa da mutane ne a sansanin alhazai da ke Abuja.

Wanda ake zargin, mai suna Yahaya Zango, an bayyana cewa yana da alaka da sace-sacen mutane da dama a Abuja da Kogi.

A ranar Lahadin da ta gabata ne jami’an tsaro da suka hada da na DSS suka cafke Zango a yayin da ake tantance maniyyatan da suka nufa.

Idan za a iya tunawa, a ranar 12 ga watan Mayu, NAHCON ta kammala jigilar maniyyata mahajjata a jihohi hudu zuwa kasar Saudiyya, yayin da ake sa ran ā€˜yan Najeriya 64,188 za su halarci aikin hajjin bana.

Babban hafsan hafsoshin tsaron kasar, Christopher Musa, a ranar Juma’a, ya ce sojoji sun sayo sabbin kayan aiki domin karfafa ayyukan yaki da rashin tsaro, ciki har da sake bullar hare-haren ā€˜yan tada kayar baya.

vanguard news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar Ę“ansandan jihar Kaduna, sun buʙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ʙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ā€˜Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ʙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ā€˜yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp