A wani samame da rundunar yaki da garkuwa da jama’a ta ‘yan sandan birnin tarayyar Abuja da ke garin Rubochi na karamar hukumar Kuje ta aiwatar a kauyen Ukya da ke kan iyaka da jihar Nassarawa ta samu nasarar tseratar da wadanda masu garkuwa suka sace su 14.
Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan birnin tarayya ta fitar, rundunar ta ce sun samu nasarar ceto mutanen ne bayan kaddamar wa wurin da masu satar jama’a suke, inda kuma masu garkuwar da jama’a suka fara da bude wa ‘yan sanda wuta.
To sai dai ‘yan sandan sun ce hakan ne ya sa jami’ansu suka mayar da wutar abin da ya yi sanadiyyar kashe mai garkuwar guda daya sannan sauran suka ranta a na kare tare da raunukan harbi a jikinsu.