fidelitybank

An kubutar da Daliban jami’ar Tarayya ta Gusau su 5

Date:

An kuɓutar da ɗaliban Jami’ar Tarayya ta Gusau guda biyar cikin ɗalibai da aka sace.

Wata ƴar uwar ɗaya cikin ɗaliban da aka sace wadda ta buƙaci a sakaya sunanta, ta faɗa wa BBC cewa a ranar Asabar ne ƴar uwarta da aka sace ta kira ta a waya take faɗa mata cewa sun samu kuɓuta suna Abuja.

“Ta faɗa mana cewa an ɗauko su ne daga dajin birnin Gwari inda aka kawo su bakin titi aka damƙa su ga sojoji. Ta ce su tara aka dawo da su, inda sauran na can a hannun ƴan bindiga,” in ji ƴar uwar ɗalibar.

Ta ce suna farin ciki da dawowar ƴar uwarsu da kuma saura da aka saki bayan shafe sama da watanni biyar a hannun ƴan bindiga.

Har ila yau, ƴar uwar ɗaya daga cikin ɗaliban da suka kuɓuta, ta ce ƴar uwar tasu a faɗa musu cewa ƴan bindigar sun lakaɗa musu duka, tare da ba su masara kawai.

Ta ce akwai ƴan mata guda uku da suka yi yunkurin tserewa har sau biyu ana kama su, inda ɗaya daga cikinsu ma ba ta da lafiya a yanzu.

“Ta ce suna ɗa yawa sun kai su kusan 40, amma a hankali wasu na ta guduwa. Ba su sani ba waɗanda suka gudu sun samu komawa gida ko kuma an kashe su a hanya ba,” kamar yadda ƴar uwar ɗalibai ta shaida wa BBC.

Ta ce cikin mutum tara da aka saki yanzu sun kunshi ɗalibai mata biyar na jami’ar, inda saura huɗu kuma suka kasance leburori.

the sun news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp