Ragowar mutane uku da aka yi garkuwa da su a Isanlu-Isin, karamar hukumar Isin ta jihar Kwara sun samu ‘yanci.
Sakin nasu a daren ranar Asabar bayan kwana biyu da sace su, ya biyo bayan matsin lambar da dakarun rundunar ‘yan sandan jihar da kuma ‘yan banga karkashin jagorancin kwamishinan ‘yan sanda, Ebunoluwarotimi Adelesi suka yi wa masu garkuwar.
An yi garkuwa da Dipe Ajayi, Kunle Abolarin, Femi Abolarin da Femi Ajayi a ranar Alhamis a Isanlu-Isin da kimanin awa 1700 kamar yadda rahotannin ‘yan sanda suka bayyana.
Tun da farko tawagar ‘yan sanda da mafarauta da ‘yan banga sun kubutar da biyu daga cikin wadanda lamarin ya shafa, Oke Olatunji da Femi Ajayi a ranar Asabar da ta gabata a wani dajin da ke yankin Isin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Okasanmi Ajayi, a Ilorin a ranar Lahadi, ya bayyana cewa kwamishinan ‘yan sandan da kan sa ya jagoranci aikin bincike da ceto wadanda aka sace.


