Akalla ‘yan Najeriya 150 ne aka mayar kasarsu jiya Talata daga Yamai babban birnin Nijar, inda hukumar bayar da gajin gaggawa ta karbe su a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Lagos.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, mutanen wadanda suka koma gida don radin kansu sun sauka ne a wani jirgin sama da aka yi shatarsa na kasar Mali da kusan karfe 11:20 na safe.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya da hadin guiwar hukumar shige da fice ta Najeriya da sauran hukumomi na Najeriya suka shirya mayar da mutanen kasar tasu.
Mutanen sun hada da maza 98 da yara maza 11 da kananan yara maza biyu sai mata manya 24 da yara maza 13 da kuma jarirai mata biyu.