Firaministan Birtaniya ya kori Suella Braverman daga muƙaminta na sakatariyar harkokin cikin gida game da wata maƙala da ta saɓa wa fadar gwamnatin kan zargin ‘yan sanda da nuna son-kai a harkar zanga-zanga.
An zargi Mrs Braverman da ingiza tashin hankali a maƙalar da ta rubuta gabanin gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayan Falasɗinawa a Landan a ƙarshen mako, inda aka yi arangama tsakanin masu macin da ‘yan sanda.
An kore ta ne da safiyar Litinin ɗin nan, kamar yadda wata majiya ta shaida wa BBC. Ba a bayyana sunan wanda zai maye gurbinta ba tukunna.
An ga Sakataren Harkokin Waje James Cleverly na shiga Fadar Downing Street a safiyar Litinin kuma ana raɗe-raɗin cewa shi ne zai maye gurbinta a matsayin sakataren harkokin cikin gida.
Haka nan, an ga tsohon firaminista David Cameron ma ya shiga fadar, abin da ya sa ake zaton zai koma gwamnati a matsayin sakataren harkokin waje.