‘Yan wasa daga Rasha da Belarus ba za su shiga gasar tsalle-tsalle ba ta nakasassu wato Paralympics ta 2022 da za a gudanar a ƙasar China.
Kwamitin kula da gasar tsalle-tsalle da guje-guje ta nakasassu ta yanke hukuncin ne, sakamakon yaƙin da ƙasashensu suka ƙaddamar kan Ukraine a makon da ya gabata.
Da ma tuni a ka shaida musu cewa, ba za su shiga gasar da tutocin ƙasashen nasu ba, sai dai a matsayin masu zaman kansu, kafin daga baya a dakatar da su baki ɗaya.
Tuni dai sauron hukumomin wasa daban-daban suka dakatar da ƙungiyoyin da kuma ƙasar ta Rasha.