Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya kori babban hafsan ‘yan sandan kasar Laftanar Janar Majak Akec Malok daga mukaminsa, a wani mataki na hukunta jami’an tsaron bayan samun rahotannin yuƙurin yi masa juyin mulki
Shugaban ya sanar da maye gurbinsa a gidan talabijin na kasar, inda ya nada Laftanar Janar Atem Marol Biar a matsayin sabon shugaban ‘yan sanda.
A ranar 11 ga watan Nuwamba ne aka fara yada jita-jitar juyin mulkin, yayin da Shugaba Kiir ke birnin Riyadh don halartar taron Saudiyya da Afirka.
Washegari, rahotonni sun ce an kama jami’an soji da na leken asiri 27.
Ƙasar ta gabashin Afirka da ke shirin gudanar da zabenta na farko tun bayan samun ‘yancin kai a shekara ta 2011, na fuskantar sauye-sauyen tsaro da aka dade ana jira.
A halin da ake ciki kuma, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ya kara wa’adin dakarun wanzar da zaman lafiya a yankin Abyei da ake takaddama a kai na tsawon shekara guda.


