An kori Sufeto na ‘yan sanda, Ubi Ebri, wanda ya harbe wani matashi a kwanan baya a garin Asaba da ke jihar Delta daga aikin ‘yan sandan Najeriya NPF.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe ne ya bayyana hakan.
Kakakin ‘yan sandan ya ce, za a gurfanar da Sufeto Ebri gaban kotu a yau Laraba.
Sufeto Ebri a yayin da yake takawa da bincike na yau da kullun, ya harbe matashin har lahira sannan ya gudu tare da abokan aikinsa.