Rundunar ‘yan sandan Jihar Legas, ta sallami wani jami’inta, Kofur Opeyemi Kadiri, saboda binciken wayar wani matafiyi.
Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce an sallami kofur ɗin ne bayan na’urar daukar bidiyo ta nuna shi yana binciken wayar mutumin a gefen hanya wanda kuma hakan ya saba wa umarnin da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Usman Alkali Baba ya bayar.
A cikin bidiyon, an jiyo matafiyin na kokawa da nuna rashin amincewa kan bukatar da dan sandan ya yi na binciken wayarsa, inda ya ce sufeton ‘yan sandan kasar ya hana yin hakan, amma jami’in ya ki saurara masa.
Kofur Kadiri na aiki ne da rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta shiyyar Dolphin.
Hukumar ‘yan sanda, ta gargadi jami’anta da cewa su tabbatar sun nuna kwarewa da kuma yin abin da doka ta tanada yayin gudanar da ayyukansu, sannan ta kira jama’a su dinga bai wa ‘yan sandan hadin kai yayin gudanar da aikinsu.


