fidelitybank

An kori ƴan sanda bakwai daga bakin aiki

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Imo, ta kori jami’anta bakwai waɗanda aka samu da laifukan da suka ƙunshi cutar da al’umma da razanarwa da yi wa jama’a ƙwacen kuɗi, da bincikar wayoyin jama’a ba bisa ƙa’ida ba, tare kuma da saɓa wa umarnin babban Sifeton ‘yan sanda na ƙasar kan kyakkyawar mu’amala da sauran al’umma.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Mike Abattam ya fitar, ya ce an kama jami’an ne ranar 8 ga watan Nuwamban 2022 a harabar wani banki da ke birnin Umuahia na jihar Abia, a lokacin da suke tsaka da aikata munanan laifukan karɓar kuɗi a wajen mutanen da ba su aikata wani laifi ba.

Ya ƙara da cewa an gurfanar da su a gaban kotun Majistare da ke birnin Owerri, inda aka same su da laifi, inda kuma nan take rundunar da kore su daga bakin aiki.

Mista Abattam ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bayar da umarni ga duka shugabannin ofisoshin ‘yan sanda da ke faɗin jihar da su tabbatar da cewa sun gargaɗi jami’an da ke aiki a ƙarƙashinsu kan aikata makamancin wannan laifi,.

Yana mai cewa duk jami’in ɗan sandan da aka samu da hannu a irin wannan laifi to zai fuskanci matakin ladabtarwa.

tribune news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An ceto Mutane 25 da syka kife a kwale-kwalen Sokoto

Hukumomi a jihar Sokoto sun ce, sun samu nasarar...

An fara duba rabon gyaran arzikin Najeriya

Shugaban Hukumar rarraba arziƙin ƙasa RMAFC, Mohammed Shehu, ya...

Kwallaye 6 da aka zurawa Santos a raga ta sanya Neymar ya fashe da kuka

Ɗan wasan tawagar Brazil, Neymar ya fice daga cikin...

Hukumar Shari’a ta magantu kan sadakin dubu 20 da ya yamutsa hazo a Kano

Hukumar shari’a ta jihar Kano, ta ce ba a...

Cutar Mashako ta yi ajalin Yara hudu a Kano

Rahotanni na cewa cutar mashaƙo wadda aka fi sani...

Cin zaben da NNPP ta yi a Kano cuwa-cuwa ne – Ata

Ministan Jiha na Gidaje da Cigaban Birane, Rt Hon...

Mutane kusan 40 sun ɓace sakamakon haɗarin kwale-kwale a Sokoto

Aƙalla mutum 40 ne ake nema bayan haɗarin kwale-kwale...

APC ta yi kwaf daya a zaben cike gurbin Kaduna da Jigawa

Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Jigawa ta yi...

Ba mu yarda da zaben Ghari da Tsanyawa ba – NNPP

Jam'iyar NNPP mai mulkin jihar Kano a arewacin Najeriya...

QPC ta nemi INEC ta soke zaɓen Kano

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta nemi hukumar zaɓe...

Zaɓen Kano: An kama Mutane 288 da tayar da zaune tsaye

Rudunar ƴansandan jihar Kano, ta sanar da kama mutum...

An Kama wakilin jam’iyya da Naira miliyan 25.9 na Siyan Kuri’a

Jami’an tsaro sun kama wani da ake zargin wakilin...
X whatsapp