fidelitybank

An kori Ɗan Sandan da ya ci zalin farar hula

Date:

Hukumar ƴan sanda, ta kori daya daga cikin ma’aikatanta, saboda cin zalin wani farar hula.

Jami’in mai suna Liyomo Okai da ke aiki a babban ofishin ƴan sanda na Ekori a Jihar Rivers, an gan shi ne a wani bidiyo na ranar 31 ga watan Yuli yana dukan wani mutum da adda.

Rundunar ƴan sandan ta sanar da hakan ne a shafinta na Tuwita a jiya da yamma.

Ta kuma ce, korar jami’in ta zai fara aiki nan take daga ranar 8 ga watan Agusta.

Sifeto Janar na ƴan sanda IGP Usman Alkali Baba psc(+), NPM, fdc, ya bayyana matukar takaicinsa akan rahoton cin zali da ƙwace da ake tuhumar wasu ƴan sanda a ƙorafe-ƙorafen da jama’a suka gabatar a kafafe daban-daban da aka gabatar, har da waɗanda ake yi a shafukan sada zumunta.

Babban sufeton ƴan sandan ya kuma bai wa duka kwamishinonin hukumar umarnin tabbatar da sa ido sosai da kula da ayyukan jami’anta kan faruwar irin waɗannan abubuwa.  In ji BBC.

nigerian 
news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Hogan ya mutu bisa cutar gazawar koda

An bayyana cikakkun bayanai game da mutuwar ɗan wasan...

Sojoji sun kashe rikaken dan Bindiga Dan Dari Biyar a Sokoto

Dakarun Operation FANSAR YANMA sun yi nasarar fatattakar wani...

An kashe utane 30 a yakin Thailand da Cambodia

An shiga kwana na uku na faɗan kan iyaka...

Ba mu ƙayyade shekarun shiga ƙaramar sakandare JSS1 – Ma’aikatar Ilimi

Ma'aikatar Ilimi a Najeriya ta musanta rahoton da wasu...

Ido da Ido na ga yadda Sojojin Isra’ila ke kashe Falasdinawa – Tsohon Sojin Amurka

Wani tsohon sojan Amurk ya ce, ya ga yadda...

‘Yan majalisar Birtaniya 220 na neman ƙasar ta amice da ƙasar Falasɗinu

'Yan majalisar Birtaniya 220 sun nemi gwamnatin ƙasar ta...

Buhari yaki karbar kyautar Agogon lu’u-lu’u da jirgin sama – Garba Shehu

Mai magana da yawun tsohon Shugaban Najeriya Muhammad Buhari,...

An kama wanda ya kashe tsohuwar Matarsa a Jigawa

Ƴansandan Jihar Jigawa sun ce, sun kama wani mutum...

Fadar shugaban kasa ta mayar da martani kan Kwankwaso

Fadar shugaban kasa, ta mayar wa tsohon gwamnan Kano...

Barau FC ta naɗa Ladan Bosso sabon kocinta

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC ta sanar da...

Am fara dawo da ‘yan Najeriya daga Afrika ta Tsakiya

Hukumomi a Najeriya sun ce, sun fara ƙoƙarin mayar...

G-Fresh da Hamisu Breaker sun samu gurbi kurkuku bayan sun watsa Naira

Babbar kotun tarayya da ke jihar Kano ɗaure shahararrun...
X whatsapp