Hukumar kula da aikin ‘yan sanda ta ƙasa, ta amince da korar wasu jami’anta bakwai bisa laifin amfani da aiki ta hanyar da ba ta dace ba.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Ikechukwu Ani ya fitar, ya ce hukumar ta dauki matakin ne a zamanta na 21 karkashin jagorancin Justice Clara Ogunbiyi a madadin shugaban hukumar, Solomon Arase.
Sanarwar ta kuma ce, baya ga korar jami’an bakwai an kuma ladabtar da wasu jami’an tara ta hanyar rage musu girman muƙami.