Wasu gungun mutane a ranar Asabar sun kashe wani dan banga Lugbe dake birnin tarayyar Abuja, bisa zargin yin kalaman batanci ga fiyayyen Halitta.
An tattaro cewa, ’yan kungiyar ’yan banga da ke gadin kasuwar Timber shed da ke rukunin gidajen gwamnatin tarayya da ke Abuja sun so kama wasu mazauna kasuwar da ke yawo a kasuwar da sanyin safiyar Asabar.
An ce mazauna garin sun roki ‘yan banga da su ‘yanto su cikin ikon Allah, amma abun ya ci tura.
Wani dan kasuwa a kasuwar ya ce, an yi wa dan bangan duka tare da jefe shi kafin a kona shi.
Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da cewa an yi wa dan banga dukan tsiya tare da jefe shi kafin ’yan iskan su kona shi.