fidelitybank

An kkama likitan bogi da ya ke karbar haihuwa a Kano

Date:

Sama da cibiyoyin kiwon lafiya dari da shagunan masu sayar da magani aka rufe a karamar hukumar Tudunwada da ke jihar Kano, ciki har da asibitin da wani likitan tiyata na jabu da ake haihuwa a asibitin.

Rufewa da kame masu gidajen ya biyo bayan rahotannin mutuwar mata da dama yayin da suke haihuwa da kuma marasa lafiya da suka samu nakasu bayan amfani da cibiyoyin kiwon lafiya.

Karamar hukumar, ta damu da ci gaban da aka samu ta kafa kwamitin lafiya karkashin jagorancin wani shugaban al’umma, Abubakar Usman Kareba wanda ya binciki lamarin tare da bankado dimbin cibiyoyin kiwon lafiya na bogi da ke aiki ba bisa ka’ida ba a yankin.

Kareba ya shaidawa manema labarai cewa bayan rufe cibiyoyin kiwon lafiya na jabu, an kama ma’aikatansu.

Ya ce karamar hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen daukar tsauraran matakai na shari’a a kan duk wadanda aka kama, daga ciki akwai ma’aikacin likitancin gargajiya amma yana haihuwar mata jarirai tare da yin aikin tiyata.

Likitan na jabu, James Bawa wanda dan jihar Kaduna ne, ya amince cewa, yana da laifukan da ake tuhumarsa da shi, amma ya nemi kwamitin da ya yafe masa tare da alkawarin komawa jiharsa.

Wani mai suna Malam Shehu, mai kula da magungunan gargajiya, ya yarda cewa ya dade yana aikin tiyata a yankin, kuma yana yi wa marasa lafiya allura da karbar mata masu nakuda.

Shugaban Kwamitin, Abubakar Usman Kareba ya bada tabbacin cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen daukar matakin shari’a a kan duk wadanda aka kama da nufin hana wasu.

breaking news in nigeria today 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp