Jami’an tsaro sun ce sun kashe aƙalla ‘yan bindiga 23 a ƙaramar hukumar Danko-Wasuguta jihar Kebbi cikin makon nan, tare da kuɓutar da wasu mutanen da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su.
Bayanai dai na nuna cewa hukumomin tsaro tare da hadin gwiwar ‘yan ƙungiyoyin sintiri sun fara yin aiki tare wajen ganin sun kakkabe ‘yan bindiga da ke tsallakawa daga jihohi masu makwabtaka domin addabar yankunan jihar ta Kebbi.
Hon Hussaini Bena shi ne shugaban ƙaramar hukumar Danko-Wasugu. Ga kuma ƙarin hasken da ya yi wa Usman Minjibir dangane da wannan nasara.


