Jami’an tsaro a Anambra sun kashe wani da ake zargin dan kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB ne, tare da raunata wasu mutane uku da ke kokarin tilasta zaman dirshen a jihar.
Rundunar ‘yan sandan jihar a cikin wata sanarwa da kakakinta, Ikenga Tochukwu ya fitar, ta ce an kama ‘yan kungiyar ta IPOB ne a lokacin da suke aiki a kan babur kafin su bude wuta.
Ikenga ya ce a yayin arangamar, an kama barayin daya, yayin da sauran ukun suka yi nasarar tserewa kamawa, inda suka samu raunuka a harsashi.
Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, lamarin ya faru ne a gadar sama ta Oba, dake karamar hukumar Idemili ta kudu.
Sai dai duk da tabbacin da ‘yan sanda da jami’an tsaro suka bayar, mazauna Anambra sun zauna a gida ranar Alhamis.
An kuma lura cewa duk wata hanya a jihar babu kowa daga Awka zuwa Onitsha da Nnewi.
Hatta ma’aikatan gine-gine a Ekwulobia, da Gwamna Chukwuma Soludo ya yi aikin gadar sama da ta hada Oko, Igboukwu da Amawbia sun yi watsi da wuraren.
Babu wata kasuwa a Anambra da aka bude domin kasuwanci, ciki har da shaguna da gareji.