Mayaƙan ƙungiyar Houthi 10 aka kashe a harin da suka yi yunƙurin kai wa wani jirgin ruwan dakon kaya a Tekun Maliya, a cewar rahoton kamfanin labarai na AFP.
Sojojin ruwan Amurka ne suka lalata ƙananan jiragen ruwan ƴan tawayen na Houthi da suka yi yunkurin shiga jirgin ruwan.
Jiragen ruwa huɗu daga yankunan da ‘yan Houthi ke iko da su a Yemen sun yi lugudan wuta kan jirgin Maersk Hangzhou, inda suka kai har kusa da jirgin, in ji rundunar sojin Amurka.
Jirage masu saukar ungulu daga jirgin yaƙin Amurka sun yi wa jiragen na ƴan Houthi luguden wuta tare da lalata uku ta hanyar nutsar da su cikin ruwa.
An kashe ma’aikatan jiragen sannan jirgi na huɗu ya tsere daga yankin.
Tun a watan Nuwamba ne ‘yan Houthi suke kai hare-hare kan jiragen ruwa a tekun Bahar Rum.
Ƙungiyar ‘yan tawayen ta Yemen da ke samun goyon bayan Iran ta yi iƙirarin cewa hare-haren da ta kai kan muhimmin hanyar sufurin jiragen ruwa na kan jiragen ruwa da ke da alaka da Isra’ilan ne, a matsayin martani ga yaƙin Gaza.