Dakarun haɗin gwiwa da ke yaƙar Boko Haram – MNJTF ƙarƙashin rundunar ta ɗaya da ke garin Mora a Kamaru sun kashe mayaƙan Boko Haram uku a sumame daban-daban da suka kai a Zigue da Soueram a ranakun 15 da kuma 22 na watan Afrilun 2024.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar soji, Leftenar Kanar Abubakar Abdullahi ya sanyawa hannu ta ce a harin farkon na ranar 15 ya faru ne a garin Zigue da ke iyakar Kamaru wanda ya yi sanadiyyar kashe ɗan boko haram ɗaya.
Hari na biyu ya faru a safiyar ranar 22 a garin Soueram da ke kusa da iyakar Kamaru da Najeriya inda dakarun suka yi nasarar kashe wasu mayaƙan Boko Haram guda biyu.
Yayin sumamen an gano bindigar PKM guda ɗaya da AK-47 ɗaya da alburusai 5 da kuma harsasai guda 20.
Sanarwar ta ce dakarun sun ci gaba da nuna jin daɗinsu kan yadda mazauna garuruwan ke basu goyon baya da kuma samar masu da bayanai wanda ya taimaka masu wajen cimma nasarorin.
Ya ce “muna neman al’umomi su ci gaba da bamu goyon baya kuma MNJTF za ta ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da tsaro a tafkin Chadi da ƙara ƙarfafa murƙushe ayyukan ta’addanci a yankin”.