fidelitybank

An kashe wani Matashi a kan faɗan Kare

Date:

Wasu ‘yan ta’adda a jihar Bauchi sun kashe wani mutum mai suna Peter tare da raunata wani Dokagk Danladi mai shekaru 38 da haifuwa, bisa zargin satar karnuka.

An kai harin ne a daren ranar 9 ga watan Afrilu a yankin Lushi da ke jihar.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, 10 ga watan Afrilu, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakil, ya ce, “Mutane biyun da aka kashe an zarge su ne da laifin satar kare kuma wasu fusatattun matasa sun kai musu hari da misalin karfe 11:30 na rana.

A cewar Wakil, an kashe Peter ne a wurin, yayin da Danladi ya samu raunuka da dama a kai, inda aka garzaya da shi asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa domin samun kulawar gaggawa.

Tawagar ‘yan sanda karkashin jagorancin jami’in ‘yan sandan yankin sun ziyarci wurin domin tattara shaidu da kuma bin diddigin wadanda suka kai harin.

Wakil ya tabbatar wa da jama’a cewa ana gudanar da cikakken bincike, inda ya ce, “Hukumar ba za ta bar wani abu ba wajen hukunta duk wanda ya aikata laifin.”

Da yake yin Allah wadai da harin, kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya bayyana wannan aika-aika a matsayin “batsa” da kuma “mummunar cin fuska ga bin doka da oda.

Ya nanata cewa babu wani dan kasa da ke da hakkin daukar doka a hannunsu.

Aliyu ya kara da cewa, “Komai laifin da ake zargin, dole ne a mika wadanda ake tuhuma ga hukumomin tsaro domin bin ka’ida.

Ya kuma tabbatar wa mazauna garin cewa ‘yan sanda na ci gaba da jajircewa wajen ganin ba a sake aukuwar irin wadannan abubuwan da suka sabawa doka ba, yana mai kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da baiwa hukumomi hadin kai yayin da ake ci gaba da bincike.

vgn

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...
X whatsapp