Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta ce jami’anta sun yi nasarar kashe wani da ake zargin dan fashi da makami mai suna Ifienyichukwu Ilegalu a yankin Mararaba da ke karamar hukumar Karu a wani samame na fashi da makami.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, DSP Ramhan Nansel, ya bayyana a wata sanarwa a ranar Asabar cewa an kama wani Edache Joseph, wanda ke cikin ‘yan fashin.
Ramhan Nansel ya bayyana cewa kama shi ya biyo bayan matakin da kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Umar Shehu Nadada, ya yi na yin kwaskwarima ga tsarin aikin ‘yan sanda na yankin Maraba, inda a baya-bayan nan aka samu rahotannin faruwar al’amura na fashi da makami.
Ya ce rundunar ta samu bayanai ne a ranar 5 ga watan Afrilu cewa, wasu gungun ‘yan fashi da makami 8 ne suka far wa wasu mazauna unguwar Aso pada da ke yankin Mararaba.
Sanarwar ta ce, bayan samun bayanan ne jami’an ‘yan sanda tare da hadin gwiwar ‘yan banga da wasu jajirtattun jama’ar yankin suka bi sawun ‘yan ta’addan, lamarin da ya kai ga kashe wani da ake zargin tare da kama wani.
“Wanda ake zargin ya yi bayani mai amfani, kuma yana taimaka wa ‘yan sanda wajen gudanar da bincike.
“Kwamishanan ‘yan sandan ya yabawa kokarin jami’an ‘yan sanda, kungiyar ‘yan banga, da sauran al’umma bisa bajintar da suka nuna, ya kuma ba su tabbacin ci gaba da ba su goyon baya. Ya kuma umurci sauran jama’a da su ba ‘yan sanda hadin kai domin kawar da masu aikata laifuka a jihar,” in ji sanarwar.