An shiga kwana na uku na faɗan kan iyaka tsakanin Thailand da Cambodia.
Sojojin Thailand sun ce Cambodia ta kai musu hari a yankunansu da ke kusa da gaɓar teku ta kudanci, sai dai sun fuskanci turjiya daga sojojin ruwan da suka fatattake su.
Sama da mutum 30 aka kashe sannan dubbai suka tsere daga muhallansu tun bayan soma wannan rikici a ranar Alhamis, yayin da kowanne ɓangare ke cewa ba shi sarara wa juna.
Cambodia ta faɗa wa kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) cewa tana son a gaggauta tsagaita wuta ba tare da sharuɗɗa ba.
Amma wakilin BBC a Bangkok ya ce ba wannan ne a gaban Thailand ba.