Hukumar Sadarwa ta ƙasa (NCC) ta lura cewa, ‘yan Najeriya da sauran ‘yan kasar a cikin Najeriya a shekarar 2021 sun kashe Naira tirilyan 3.25 wajen yin amfani da lokacin, bayanai, da sauran ayyukan sadarwa.
A shekarar 2020, an kashe Nairavtirilyan 2.88, yayin da a shekarar 2019 aka kashe Naira tirilyan 2.47, akan bayanai da sauran ayyuka.
Wani rahoto mai suna, ‘Rahoton Shekara-shekara na Subscriber/Network Data,’ da Hukumar NCC ta fitar, ya ce, “Wannan hada-hadar ta dogara ne kan bayanan da aka samu daga masu ba da sabis. Ya nuna cewa, jimillar kudaden shiga da aka samu a fannin ya kai Naira tirilyan 3.25.”
A shekarar 2021, an yi ta kiraye-kirayen mintuna biliyan 173.56 a Najeriya, wanda hakan ya nuna an samu karuwar kashi 15.07 cikin 100 daga cikin mintuna biliyan 150.83 na kiran waya da aka yi a shekarar 2020.
Adadin sakonnin SMS da aka aika ya karu da kashi 15.06 daga biliyan 8.22 a shekarar 2020 zuwa biliyan 9.46 a shekarar 2021.
Masu aiki a GSM ne suka samar da kudaden shiga, kafaffen waya, samar da sabis na Intanet, ƙarin sabis na ƙima, haɗin kai da raba kayan more rayuwa, da sauran wurare.
Hukumar NCC ta bayyana cewa, masu amfani da GSM sun samu kashi 85.42 cikin 100 na kudaden shigar da ake samu a fannin sadarwa.
NCC ta ci gaba da cewa, dakatar da tallace-tallace da rajistar sabbin SIMs, musayar SIM, da ayyukan jigilar kayayyaki ya shafi ci gaban masu amfani da shi a fannin.