Rahotanni sun ce ana ci gaba da gwabza kazamin faɗa a babban birnin ƙasar Sudan, Khartoum, da kuma yankin Darfur da ke yammacin ƙasar.
Rahotannin sun kuma ce an kashe ɗaruruwan mutane a faɗan da ake ci gaba da yi.
Shaidu sun bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa gawawwakin mutane sun cika kan titunan birnin Omdurman a ranar Alhamis, a wani sabon rikici da ya ɓarke tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF.
“Gawawwakin mutane sanye da kakin soji sun cika kan titunan tsakiyar birnin bayan faɗa a jiya,” kamar yadda wani shaida ya ruwaito.
Hukumar kula da masu ƙaura ta duniya (IOM) ta ce an kashe mutane 700 a rikici a yammacin Darfur.
An kuma ruwaito ɓacewar mutane sama da 300 bayan kazamin faɗa da aka yi a birnin El Geneina.
Shaidu sun zargi dakarun RSF da kai wa waɗanda ba larabawa hari da kuma kashe su a rikicin.
Ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Khartoum ya ce ya damu matuka da rahotannin da shaidu suka bayar na cin zarafin bil adama da RSF da kuma wasu mayaka ke yi.
Sai dai RSF ta ce ba ta da hannu a abin da ta bayyana a matsayin “rikicin kabilanci”.
Dubban mutane ne suka tsallaka zuwa ƙasar Chadi a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata domin samun tsira.
Kusan mutane miliyan shida ne aka tilastawa barin gidajensu tun lokacin da yaƙin ya ɓarke a tsakiyar watan Afrilu.