fidelitybank

An kashe Soja tare da jikkata wa su a Kaduna

Date:

Wasu mahara dauke da makamai sun kai wa sojoji biyu na bataliya ta 312 Barrack Kalapanzi hari a Babar Saura a jihar Kaduna.

Zagazola Makama, kwararre kan yaki da tada kayar baya da ya mayar da hankali kan yankin tafkin Chadi, ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a hannunsa na X.

Makama ya bayyana cewa wasu majiyoyin leken asiri ne suka sanar da shi cewa wasu maharan uku dauke da manyan muggan makamai ne suka bindige sojojin, inda daya daga cikinsu mai suna Kofur James (wanda ba a san sunan sa ba) ya mutu, sannan kuma Private Ibrahim Bazalla ya jikkata.

Masanin tsaro ya bayyana cewa maharan sun sace bindigogin AK-47 guda biyu daga hannun sojojin kafin daga bisani su arce daga wurin.

Rahoton ya ce, an garzaya da wadanda harin ya rutsa da su zuwa Asibitin Reference na Sojoji 44, inda aka tabbatar da mutuwar Kofur James, yayin da Private Bazalla ke samun kulawar jinyar raunin da ya samu.

Makama ya bayyana cewa an bi sahun maharan ne zuwa Degel 2, Kaduna, inda suka yi watsi da wata mota kirar Toyota Corolla ta azurfa, bayan wani samame na hadin gwiwa da sojoji, ‘yan sanda, da kungiyoyin ‘yan banga suka yi.

“Yayin da suke yunkurin tserewa, maharan sun kwace wata farar mota kirar Toyota Venza daga hannun wani farar hula mai suna Abdullahi Mohammed, da ke Badarawa, Kaduna.

Ya kara da cewa “ana ci gaba da kokarin kama wadanda ake zargin tare da kwato motar da aka sace.”

nasarawa news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp