Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, da sanyin safiyar Talata sun kai hari kauyen Tursa da ke karamar hukumar Rabbah a jihar Sokoto, inda suka kashe akalla mutum daya tare da yin garkuwa da mutane shida daga kauyen.
Da yake tabbatar da hakan ga manema labarai a safiyar ranar Talata a Sokoto, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Ahmed Rufa’i, ya ce lamarin ya faru ne da tsakar daren ranar Talata.
Rufa’i ya ce ‘yan bindigar sun shiga kauyen ne suka kona daki tare da kona mutum daya da ke ciki.
“Sun kuma kona babura biyu a cikin aikin tare da yin garkuwa da mutane shida yayin da wasu kuma aka yi awon gaba da wasu shanu da ba a bayyana adadinsu ba.”
Ya kuma yi alkawarin karin bayani kan lamarin daga baya, inda ya tabbatar da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bayar da umarnin farautar wadanda ake zargin.