fidelitybank

An kashe mutum guda tare da jikkata da dama a wani rikici a Bauchi

Date:

Wata hatsaniya a kauyen Zaranda da ke karamar hukumar Toro na jihar Bauci, ta janyo mutuwar mutum ɗaya da kuma jikkata wasu da dama.

Cikin wata sanawar da mai magana da yawun ƴansandan jihar, Ahmed Wakili ya fitar, ta ce an jikkata mutum uku daga garin Zaranda a rikicin.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9 na safiyar Talata, lokacin da mazauna garin suka fito domin nuna fushi kan wani mai sayar da gawayi da aka kama, kamar yadda rahotonni suka ruwaito.

Zanga-zangar da suka fito domin nuna ɓacin-ransu ta kuma saka ƙungiyar maharba da tabbatar da tsaro harba bindigogi a sama.

Wakili ya ce an garzaya da su zuwa cibiyar kiwon lafiya a garin, inda Allah ya yi wa ɗaya daga cikinsu mai suna Yahaya cikawa.

Kwamishinan ƴansanda a jihar, Auwal Muhammad, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan mutuwar Yahaya da kuma abin da wasu jami’an tsaro da ke cikin lamarin suka aikata.

“Tuni muka ɗauki mataki domin shawo kan lamarin da gudanar da bincike, sannan mu gabatar da waɗanda suka aikata wannan abu,” in ji sanarwar ƴansandan.

Sanarwar ta kuma ce an aika tawagar jami’an tsaro zuwa wurin da lamarin ya faru domin mayar da doka da oda da kuma sake buɗe hanyar da mazauna garin suka toshe.

national news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp