fidelitybank

An kashe Mutum guda a wani rikici a Kano

Date:

An tabbatar da mutuwar mutum daya tare da kona shaguna da dama bayan wani kazamin rikici da ya barke tsakanin matasa daga kauyukan Faruruwa da Tarandai a karamar hukumar Takai a jihar Kano.

Lamarin, wanda ya faru da misalin karfe 7:45 na dare. A ranar 23 ga watan Mayu yayin wata kasuwa a Faruruwa, wani manazarci kan harkokin tsaro Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a wani sakon da ya fitar ta hanyar tabbatar da sahihancin sa a ranar Lahadi.

A cewar Makama, rikicin ya samo asali ne bayan wani matashi mai shekaru 28 mai suna Sani Yunusa da ke kauyen Toho Diribo ya ziyarci budurwarsa a garin Tarandai.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu matasa da ake zargin ‘yan kauye ne suka yi masa kwanton bauna a hanyarsa ta dawowa, inda suka kai masa hari da sanduna da yankan katako.

“Rikicin ya kai ga kone shaguna da dama a cikin kasuwar,” in ji sanarwar.

An baza jami’an tsaro cikin gaggawa zuwa yankin domin kwantar da hankula tare da hana barkewar rikici.

Majiyar ‘yan sandan ta tabbatar da cewa al’amura sun dawo daidai amma sun tabbatar da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin rikicin tare da gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika a gaban kuliya.

naija legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp