Alƙaluma na nuna cewa an kashe mutum dubu shida da ɗari takwas a watanni shida na farkon shekara ta 2025 sanadiyyar matsalar tsaro da ke addabar sassa daban-daban na ƙasar.
Hakan na ƙunshe ne a cikin rahoton kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited, mai nazari kan tsaro a Najeriya da yankin Sahel, kamar yadda shugaban kamfanin Kabiru Adamu ya bayyana a hirarsa da BBC Hausa bayan fitar da rahoton na watan shidan farko na wannan shekarar.
Jihohin da aka fi kashe mutane a ƴan tsakankanin wata shidan su ne: Jihar Zamfara da ake kashe mutum 1088, sai Neja da aka kashe 1046, sai Borno da aka kashe 981 sai Katsina da aka kashe mutum 648 sai kuma Benue da aka kashe mutum 490 a kwanakin baya, kamar yadda rahoton ya bayyana.
Najeriya na fama da matsalar ƴan fashin daji a arewa maso yammacin ƙasar da Boko Haram a Arewa maso gabas da rikicin manoma da makiyaya a Arewa ta tsakiya sai kuma na ƴan awaren Ipob a gabashin ƙasar, lamarin da ke raba hankalin rundunar sojin ƙasar.