Wasu ‘yan fashin daji sun kai hari a yankin ƙaramar hukumar Bunguɗu da ke jihar Zamfara, inda suka kashe mutum takwas tare da raunata wasu da dama.
Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun kuma kwashi dukiyar jama’a mai tarin yawa da ta haɗa da dabbobi a harin da suka kai kan garin Gada ranar Juma’a da dare.
Wani mazaunin yankin ya ce akwai mutum kusan bakwai da suka kai asibiti sakamakon raunukan da suka ji.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen Zamfara ta tabbatar wa da BBC Hausa cewa maharan sun kashe mayaƙan sa-kai shida lokacin da suka yi yunƙurin tare su bayan sun kai hare-haren.
“Allah ya ba mu sa’a mun kashe ‘yan fashin da dama kuma wasunsu sun gudu da raunuka,” in ji ASP Yazid Abubakar kakakin rundunar a Zamfara.
A jihar Katsina mai maƙwabtaka kuma, rundunar ‘yan sandan jihar ta ce ta kashe wani ƙasurgumin ɗan fashin daji a yankin Faskari.