‘Yan sanda a China sun ce an kashe mutum shida a wani harin wuka da aka kai kan makarantar yara da ke yankin Guangdong a kudu maso gabashin ƙasar.
Ƴan sanda sun ce an jikkata mutum guda sannan sun kama wani matashi ɗan shekara 25 mai suna Wu a garin Lianjiang.
Kakakin shugaban yankin da ke birnin Lianjiang (Jianjiang), ya shaida wa ƴan jarida cewa mutum uku cikin waɗanda aka kashe kananan yara ne.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito cewa wani jami’i a yankin ya ce sauran waɗanda abin ya rutsa da su sun haɗa da malami da kuma iyaye biyu. In ji BBC.
Harin ya faru ne a ranar Litinin a daidai lokacin da iyaye suka kai ‘ya’yansu makaranta.