Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane hudu tare da yin garkuwa da mataimakin shugaban karamar hukumar Bukkuyyum a jihar Zamfara, Hon. Bala Muhammad Maijidadi da wasu da dama a yankin.
Rahotanni na cewa an kai hare-haren hadin gwiwa tsakanin daren Lahadi zuwa safiyar Litinin.
Wani magidanci mai suna Nasiru Adamu ya shaidawa manema labarai ta wayar tarho a daren ranar Talata cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki unguwar Shemori dake gundumar Mada Gusau da misalin karfe 9:20 na daren Lahadi inda suka yi garkuwa da wasu mata shida.
An kuma tattaro cewa da sanyin safiyar ranar Litinin ne wasu gungun ‘yan bindiga suka kai hari a kauyen Kairu da ke gundumar Zugu, inda suka kashe wasu mutanen yankin biyu tare da yin awon gaba da wasu mutanen da ba a tantance adadinsu ba.
A garin Mada da ke gundumar Gusau, ‘yan bindigar sun far wa Hayin Bajumi, inda suka kona gidan wani Aliyu Usman.
“Gobarar ta kashe ‘ya’yansa biyu, Ishaq Aliyu mai shekaru biyar da Jafar Aliyu mai shekaru biyu.
“’Yan bindigar sun kuma yi awon gaba da matar makwabcin Usman, tare da jaririnta mai shekara daya kafin su gudu daga wurin,” majiyar ta bayyana.
Duk kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Yazeed Abubakar ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoto.