fidelitybank

An kashe mutane akalla 117, an sace wasu 130 sannan sama da 10,463 suka rasa cikin kwana 4 a Kaduna

Date:

Majalisar wakilai a ranar Alhamis, ta bukaci gwamnatin tarayya da ta umurci sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Baba, da ya tura tawagar tsaro ta musamman a yankin Birnin Gwari da Giwa na jihar Kaduna, domin magance ‘yan ta’adda da ke addabar yankin.

Majalisar ta kuma bukaci babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar, Faruk Yahaya, da babban hafsan sojin sama, Air Marshal Isiaka Oladayo Amao, da su kara kaimi wajen yaki da ‘yan ta’adda da ‘yan fashi a kasar nan.

Kudurin ya biyo bayan wata muhawara kan kudirin gaggawa na magance yawaitar hare-haren ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da kashe-kashe a fadin kananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa na jihar da dan majalisa mai wakiltar yankin, Shehu Balarabe ya yi.

Balarabe, a zauren majalisar, ya ce, an kashe mutane akalla 117, an sace wasu 130 sannan sama da 10,463 suka rasa matsugunansu a kananan hukumomin biyu tsakanin ranakun 24 zuwa 28 ga Maris.

Dan majalisar ya ce, an yi awon gaba da shanu marasa adadi yayin da aka kona gidaje da wasu kayayyaki masu daraja a lokacin da ‘yan bindigar suka kai wa mazabar sa hari.

Ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta samar da sansanonin ‘yan gudun hijira da kuma samar da kayan agaji, domin tallafawa wadanda hare-haren ya rutsa da su.

punch newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp