fidelitybank

An kashe mutane 9 a jihar Kaduna

Date:

Kimanin mutane tara (9) ne wasu da ake zargin Fulani ne suka kashe a kauyukan Ruji da Atakjeh na masarautar Atyap da ke karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewa, an kashe wani matashi a kauyen Ruji, yayin da kuma aka kashe mutane takwas a kauyen Atakjeh a daren Laraba.

An garzaya da wasu mutane uku da suka jikkata zuwa asibiti domin yi musu magani.

Ku tuna cewa, wani kauye da ke kusa da Zangon Urban, Unguwan Wakili an kai hari tare da kashe mutane kusan 17 da wasu da ake zargin Fulani ne a masarautar Atyap kwanan nan.

Shugaban kungiyar ci gaban al’umma ta Atyap (ACDA), Dr Samuel Achi ya shaidawa DAILY POST cewa, a halin yanzu al’amura sun tabarbare a kauyen Atakjeh.

Samuel ya ce, “Abin mamaki akwai jami’an tsaro kusa da kauyen da aka kashe mutane takwas, amma sun kasa kubutar da mutanen kauyen daga hannun maharan.

“Maharan sun je kauyen ne suka gudanar da aikinsu kuma suka tafi ba tare da wani shiga tsakani daga jami’an tsaro ba.”

“Kamar yadda nake magana da ku, daya bai tabbatar da adadin wadanda aka kashe da wadanda suka jikkata ba amma a halin yanzu, muna da mutum takwas da aka kashe tare da jikkata wasu uku a kauyen Atakjeh.

“Wadanda suka samu raunuka daban-daban an kai su asibiti domin yi musu magani,” in ji shi

legit news 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp