Rahotonni daga jihar Filato na cewa ƴanbindiga sun kai harin kwanto ɓauna kan wasu ƴan banga tare da kashe aƙalla 70 a wasu ƙauyukan jihar biyu.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC cewa sun gano gawarwaki 56 bayan harin.
Sai dai bayanai na cewa akwai wasu ƴan bangar da damar da yanzu ba a gani ba, waɗanda ke fargabar sun mutu.
Can ma a ƙauyen Banyun na na jihar wani mazaunin yankin ya tabbatar da kashe ƴan banga 10.
Ya ƙara da cewa maharan sun kuma ƙona gidaje da dama da dukiyoyi.
Bayanai na cewa tun bayan da hare-hare suka yawaita a wasu yankunan Wase, aka riƙa gayyato ƴan banga daga wasu yankunan jihar da ma jihar Taraba domin taimaka wa tsaron wasu ƙauyukan yankin.