Akalla mutum hudu aka kashe aka yi garkuwa da wasu shida, a lokacin da yan bindiga suka kai hari a kasuwar Jauro Manu da ke karamar hukumar Gassol a jihar Taraba.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, baya ga wadanda harin ya rutsa da su, mutane da dama sun shiga dazuka don tsira da ransu.
Wani mazauni garin ya ce shi ne hari na uku da suka fuskanta, kuma hare-haren sun yi sanadin mutuwar mutum 12.
A wani hari na daban, rahotanni sun ce an yi garkuwa da matafiya 14 a tsakanin Mutum-biyu da Wukari da misalin karfe biyu na ranar Lahadi.
Rahotanni sun kuma ce tuni yan bindigar suka nemi a basu naira miliyan 30 kafin su saki mutanen.
KARANTA WANNAN:Â ‘Yan bindiga sun kashe mutum 3 tare da kwashe mata 5 a Taraba
Mai magana da yawun rundunar yan sanda a jihar Taraba DSP Kwache Bajabu Gambo ya tabbatar da faruwar lamarin.
Arewacin Najeriya na kara fuskantar hare-haren yan bindiga, da kuma garkuwa da mutane don neman kudin fansa.


