An kashe mutum uku a wani kokarin hadin gwiwa da ‘yan sanda da sojoji suka yi na dakile wani fashin banki a unguwar Abaji da ke Abuja a ranar Alhamis.
Wata sanarwa da ta samu sa hannun jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ƴan sanda a birnin Abuja, SP Josephine Adeh ta fitar ranar Juma’a, ta ce rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya ta samu rahoton yunƙurin fashin ne da misalin karfe biyar na yamma.
Sanarwar ta ce jami’an ƴansanda tare da haɗin gwiwar sojoji sun garzaya wurin da lamarin ya faru inda suka daƙile harin da aka kai a lokaci.
Jami’an tsaron sun yi musayar wuta da ƴan fashin inda suka yi nasarar kama mutum uku da ake zargi.
Daga cikin wadanda suka jikkata har da ɗan sanda ɗaya da kuma shugaban ƴan fashin, dukkansu an kai su asibiti amma daga baya aka tabbatar da mutuwarsu.
Sauran wadanda suka jikkata na ci gaba da samun kulawa a asibiti.
Sanarwar ta ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin kamo sauran waɗanda ake zargi, waɗanda suka gudu da raunuka sanadiyyar harbin bindiga.