Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kauyen Magarya da ke karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.
Rahotanni na cewa an kashe mutane goma sha daya da suka hada da ‘yan sandan tafi da gidanka bakwai da farar hula hudu.
An kuma lalata motoci uku ciki har da daya na Hakimin Magarya, wanda kuma dan uwa ne ga tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara, Nasir Magarya.
An kuma tattaro cewa an kona kujeru a falon gidan tsohon kakakin.
A cewar wani mazaunin yankin, Ahmad Umar, an kona makarantar Magarya Model Primary, kuma mutane da dama sun samu raunuka daban-daban.
Ba a samu samun mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Yazid Abubakar ba, har zuwa lokacin hada wannan rahoto.