Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kai hari garin Yangtu da ke yankin karamar hukumar Takum a jihar Taraba, inda suka kashe mutum 10.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Usman Abdullahi ya tabbatar wa BBC faruwar lamarin, da ya ce ya auku a ranar Juma’a da maraice.
Ya ƙara da cewa rundunarsu tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro sun tura ƙarin jami’ai zuwa yankin domin farauto ‘yan bindigar, tare da kwantar wa jama’a hankali.
Rahotonni sun ce tun da farko maharan sun tare hanyar Takum zuwa Ussa, inda suka riƙa kashe mutane.
A baya-bayan nan jihar Taraba ta kasance cikin jihohin da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.